Tuni kuma aka maye gurbinsa da Laftana Janar Fayyad al-Ruwaili.
An kuma sallami babban hafsan sojin sama da kuma na kasa.
Sanarwar da kamfanin dillancin labaren kasar ya fitar, ta ce an tura jami'an ne ritaya.
Wannan matakin dai na zuwa a daidai lokacin da yakin da kasar ke jagoranta a kasar Yemen yaki ci yaki cinyewa.